Jiya Talata Ministan harkokin wajen kasar Netherlands Halbe Zijlstra yayi murabus, bayan da ya tabbatar da cewa yayi karya a lokacin da ya ce ya gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a shekarar 2006.
Zijlstra ya bayyana gaban majalisar dokokin kasar inda ya ce ya yanke shawarar yin murabus daga mukaminsa saboda bai kamata a ce akwai wani kwakkwanto akan “mutuncin” ministan harkokin wajen kasar ba.
Wata hudu Zijlstra yayi rike da wannan mukamin.
Firayin ministan kasar Mark Rutte ya fuskanci tambayoyi akan dalilin da ya sa bai bayyanawa jama’a wannan karyar ba duk da cewa ya san da batun makonni da dama suka gabata, Amma ya ce bai fahimci tasirin bayyana batun ba sosai.
‘Yan majalisar kasar sun jefa kuri’a nuna rashin kwarin guywa akan firayin ministan jiya Talata, amma cikin sauki ya tsallake kalubalen.