Ministan Harkokin Cikin Gidan Ukraine Ya Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Sama Da Ya Kashe Mutum 15

UKRAINE-CRISIS/RUSSIA-AIRPLANE

Yau Laraba wani jirgin sama mai saukar ungulu a wajen babban birnin kasar Ukraine, ya kashe mutane akalla 15, ciki har da ministan harkokin cikin gida Denys Monastyrsky.

WASHINGTON, D. C. - Jami’ai sun ce hatsarin ya auku ne a kusa da wata makarantar renon yara ta Brovary, wani yanki da ke gabas da Kyiv.

UKRAINE-CRISIS/ZELENSKYI-SUNAK

Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin da ya haddasa hadarin ba. Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce a cikin sakon da ya aike ta kafar sadarwa ta Telegram ya umarci hukumomi da su gudanar da bincike.

Zelenskyy ya kira hadarin "mummunan tashin hankali."

Wurinda helicoptan ya fadi a Brovary

A baya jami'ai sun ce adadin wadanda suka mutu ya kai 18.

Zelenskyy, a cikin sakonsa, ya ce akalla mutane 15 ne suka mutu duk da cewa ana ci gaba da tantance adadin wadanda suka mutu. Ya ce cikin wadanda suka mutu sun hada da yara akalla uku.

-AP/Reuters