Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zelenskyy Ya Nemi Amurka Ta Kara Tallafawa Ukraine


Lokacin da Zelenskyy yake gabatar da jawabinsa a gaban gamayyar Majalisar dokokin Amurka ranar Laraba
Lokacin da Zelenskyy yake gabatar da jawabinsa a gaban gamayyar Majalisar dokokin Amurka ranar Laraba

Gabanin jawabin nasa a gaban majalisar dokokin Amurka, Zelenskyy ya gana da Shugaba Joe Biden a fadar White House a ranar Laraba.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya gabatar da jawabinsa a gaban gamayyar Majalisar Dokokin Amurka, inda ya kara mika kokon baransa na neman karin tallafin makamai.

Wannan lamari ya yi daidai da abin da tsohon Firaiministan Birtaniya Winston Churchill ya yi shekaru 80 da suka gabata, lokacin da shi ma ya yi majalisar jawabi makamancin wannan.

Ziyarar ta Zelenskyy a Washington na zuwa ne yayin da kasar ke fama da hare-haren da Rasha ke kai wa kasarsa inda yake neman kasashen duniya su tallafa don ya kara kasarsa.

“Ukraine na ci gaba da jajircewa wajen kare kanta, kuma ba za ta taba mika wuya ba.” Zelenskyy ya fadawa Majalisar Dokokin Amurka, a jawabin wanda ya yi kamanni da wanda Winston Churchill ya yi, lamarin da ya sa har ‘yan majalisar suka jinjina masa.

A farkon shekarar nan Zelenskyy ya yi makamancin wannan jawabi a zauren majalisar wakilan Birtaniya ta kafar bidiyo inda ya tabo batun jawabin da Churchill ya yi, tare da shan alwashin ci gaba da “fada ko a daji, ko a fili ko a gabar ruwa ko a titi.”

Yayin da yake nasa jawabin, shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawan Amurka Chuck Schumer, ya fadawa Zelenskyy cewa, daidai inda ya tsaya ya gabatar da jawabinsa, a nan Winston Churchill shi ma ya gabatar da nasa jawabin.

Gabanin jawabin nasa a gaban majalisar dokokin Amurka, Zelenskyy ya gana da Shugaba Joe Biden a fadar White House a ranar Laraba.

XS
SM
MD
LG