Ministan Cikin Gidan Nijar Ya Yi Barazanar Hukunta Shugabannin Kananan Hukumomi

Janar Mohamed Toumba

Ma’aikatar cikin gidan Nijar ta umurci gwamnoni su zuba ido kan ayyukan tantance mutanen da zasu wakilci al’umomin kananan hukumomi a babban taron kasa da ke tafe, da nufin tattaunawa kan sabuwar turbar da ya kamata a dora kasar bayan shekaru sama da 30 da kafa dimokradiyya a kasar.

A takardar da ya aika zuwa jihohi, Ministan cikin gida Janar Mohamed Toumba ya nuna rashin gamsuwa da yadda wasu magadan gari ke kauce wa ka’ida wajen tantance wakilan babban taron muhawara da zai tattara ‘yan kasa a nan gaba a birnin Yamai, inda aka lura da alamomin son rai a wannan al’amari na neman mafitar halin da kasa ta tsinci kanta ciki.

A saboda haka ne ya umurci gwamnoni su dauki mataki don ganin komai ya gudana cikin yanayin adalci da gaskiya. Abin da kuma shugaban kungiyar magadan gari na jihar Maradi Sadissou Sani ya yaba da shi.

Ministan, a wannan takardar sakon ya yi barazanar zartar da hukuncin da dokokin kananan hukumomi suka yi tanadi ga duk wadanda aka samu da yin fatali da ka’ida da masu yunkurin yi wa tsare-tsaren taron na Dialogue National kafar angulu.

To sai dai Shugaban kungiyar Voix des sans Voix Nassirou Saidou, na cewa mafi kyau shine a yi sabon zubi domin cimma burin da aka sa gaba a wannan sabuwar tafiya ta kasa.

A makwannin farkon juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli ne ma’aikatar cikin gida ta ankarar da magadan gari cewa a bisa tsarin dokar kananan hukumomi matakin rushe hukumomin jamhuriya ta 7 da majalissar CNSP ta dauka bai shafe su ba, saboda haka aka umurce su akan aiki, sai dai tun a wancan lokaci wasu ‘yan kasa suka nuna rashin gamsuwa da wannan tsari kasancewar magadan gari an zabe su ne a karkashin inuwar jam’iyyun siyasa .

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Ministan Cikin Gidan Nijar Ya Yi Barazanar Hukunta Shugabannin Kananan Hukumomi