To sai dai Kungiyar Masu Larura ta Musamman ta Kasa ta ce za ta kalubalanci wannan doka a kotu idan haka ya faru, akan ko mene ne dokar kasa ta ce a game da ‘yancin mabarata.
Shugaban Kungiyar, Kwamred Yarima Suleiman ya ce kungiyar za ta dauki mataki domin Ministan bai zauna da su ba, kuma bai tuntubi Hukumar Kula Da Masu Larura ta Musamman ba.
Yarima ya ce abin da ya kamata Minista ya yi shi ne, ya yi wa masu larura ta musamman tanadin abubuwa masu tsoka kamar a basu bashi domin su yi kasuwanci, ko kuma a gina su ta fannin koyar wasu sana'o'i, ko kuma a wadata su da abinci ko hanyan samun abincin cikin sauki.
Yarima kara da cewa suna nema Minista ya janye mugun kalma na 'Informant" da ya lankaya masu, saboda yana iya sawa 'ya'yansu, suyi kyamarsu, ko kuma wadanda ke taimaka masu su kyamace su ko kungiyar ta dauki mataki kan kalaman Ministan.
Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesome Wike ya ce birnin ya zama kaman birnin mabarata, kuma wannan abin kunya ne a gare mu.
Wike ya ce duk lokacin da baki suka shigo garin, babu abin da suke fara karo da shi sai mabarata a titunan birnin, saboda haka daga yau Litinin 28 ga watan Oktoba jami'an tsaro da sauran ma'aikatan birnin za su fara diban mabarata daga kan titunan Abuja.
Wike ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunta ba, domin wasu mabarata suna baiwa 'yan ta'adda labarai, wato abin da ake cema 'Informant' a turance.
To ko mene ne kundin tsarin mulki ya tanada kan wannan hukunci da Ministan ya dauka?
Barista Mustapha Haruna Soba ya yi fashin baki cewa kundin sarin mulki ya ba mabarata dama na yin walwala a ko ina a cikin kasar, saboda haka mabarata suna iya shigar da kara a kotu inda za su kalubalanci wannan tsari da Minista Nyesome Wike ya bullo da shi.
Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya idan har Kungiyar Masu Larura ba su shirya da Minista Nyesome Wike ba.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5