Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Fafutuka Na Son a Samawa Almajirai Aikin Yi


Yayin da ake ta takaddama kan makomar almajirai a sassan Najeriya bayan da aka rika mayar da su jihohin da suka fito, masu fafutukar tabbatar da daidaito a tsakanin al’uma sun ce ba samar da ilimi ba ne kadai mafita.

Mai fafutukar neman daidaito tsakanin al’umma, Fatima Abubakar, ta bayyana cewa, fitar da tsarin bai wa almajirai ilimin boko da na arabiyya ba zai wadatar ba.

A cewarta, jajircewa wajen samawa almajiran aikin hannu domin dogaro da kai ita mafita.

Fatima Abubakar ta ba da wannan maslaha ce yayin wata hira da ta yi da VOA.

Kiran kuma na zuwa ne yayin da gwamnonin arewa cin Najeriyar suka cimma matsaya kan mataki na gaba na hana barace-barace tare da mayar da hankali a kan ilmin almajirai inda za a koma ga tsarin almajiranci na da wanda babu zancen barace-barace a ciki.

Sha’anin almajiranci a Najeriya ya zama abin kyama ga wasu al’umomin arewa har ma da kudancin kasar nan inda ake ganin cewa, wadannan almajiran sun zame musu alakakai a cikin jihohinsu.

Al’amaru sun kara dagulewa almajiran bayan bullar cutar coronavirus a Najeriya inda aka yi ta korar su, ana mayar da su jihohinsu na asali.

An dai dade ana kai ruwa rana game da batun barace-barace da almajiranci inda shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya bayyana cewa, tun kafin bullar cutar coronavirus ne kungiyar, jiga-jigan gwamnatin tarayya da malaman addinin Islama suka cimma matsaya kan magance matsalar.

Ya kara da cewa, wasu gurbatattu kan yi amfani da wadannan yara wajen aiwatar da miyagun manufofinsu.

Duk da cewa ba a fara aiwatar da sabon shirin kula da almajirai ba wani malamin addinin Islama, Suleiman Sani, ya bayyana cewa, matakin gwamnonin Arewa na bias tsari.

Kazalika, kakakin gwamnan jihar Borno, Isa Gusau, ya ce, hukunta iyaye da duk wani malamin da ya karbi yara ba tare da gidan da zai ajiye su ba shi ne mafita.

A karshe dai gwamnonin arewa sun ce za su yi iyakacin kokarinsu wajen hana bara baki daya a jihohinsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG