Miliyoyin Mutane Na Fama Da Yunwa A Yamal

Ana fama da Yunwa a Yamal

Mutanen Yamal miliyan ashirin, wato kashi biyu cikin uku na al’ummar kasar na fama da rashin abinci, sakamakon yaki da ya daidaita kasar kana ya jefata cikin talauci.

Wata sanarwar hadin gwiwar hukumar abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya(MDD) da asusun talafawa kananan yara ta MDD da kuma shirin samar da abinci na duniya, na cewa yakin kasar ya taimakawa wurin samun matsalar taimako mafi muni a duniya.

Hukumomin sun ambato jawaban masu fashin baki daga wani shiri na musammman a kan samar da abinci, shirin dake taimaka wurin bincike da tabbatar da kasashe masu fama da yunwa.

Mutane kimanin miliyan goma sha biyar da dubu dari tara ne ke fama da yunwa a Yamal a cewar nazarin hukumomin, nazarin da yace mutane miliyan ashirin basu samu isasshen abinci da ruwan sha.