Microsoft Ta Dakatar Da Kera Wayar Window 10

Kamfanin Microsoft ya tabbatar da cewa ba zai sake kera wata sabuwar wayar Window 10 ba.

A wani sako da ya kafe ta dandalin Twitter, shugaban sashen kera wayoyin zamani na kamfanin Microsoft Joe Belfiore, ya ce kirkirar wata sabuwar fasaha ta wayar zamani ba itace a gaban kamfanin yanzu ba.

Ya kuma kara da cewa shi kansa ya canza wayarsa zuwa wayar Android.

Wannan labari dai bai zo da mamaki ba ganin yadda fasahar waya ta Window 10 take barin masu amfani da ita damar yin amfani da app a wayoyinsu da kuma kwamfutocinsu, amma hakan ya kasa daurewa.

A farkon wannan shekarar ne sashen Window ya fitar da sanarwar cewa kamfanin yana aiki kirkirar wata sabuwar manhajar Window 10 da zata iya yin aiki akan kowacce irin kwafuta ba tare da sai an saka mata komai ba. Amma har yanzu shiru kamar an aika da bawa garinsu.

Your browser doesn’t support HTML5

Microsoft Ta Dakatar Da Kera Wayar Window 10 - 1'00"