Alkalin kotun tarayya na Gunduma, Emmet Sullivan, ya ce ba zai iya boye rashin jin dadinsa da damuwarsa ba kan abin da Flynn ya yi, kafin daga baya ya amince da bukatar lauyoyin Flynn na soke zaman yanke hukuncin.
Flynn ya tabbatarwa Alkali Sullivan cewa, ya sani ba karamin laifi bane ayi wa masu bincike ‘karya, lokacin da suka tambayeshi zantawarsu da jakadan Rasha na wancan lokacin a Amurka, Sergey Kislyak.
Alkalin ya fadawa Flynn cewa abin da ya aikata babban laifi ne, kuma cin amanar ‘kasa ne.
Mai bincike na musamman Robert Mueller ya bayar da shawara kan ‘dan shekaru 60 a duniya, Flynn, kuma tsohon janar na soja wanda a baya ya taba zama shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Soja, da kada a yanke masa hukuncin da zai kaishi ga gidan yari, saboda irin hadin kan da yake baiwa binciken da yake gudanarwa kan alakar kwamitin kamfen din Trump da Rasha, da kuma ko Trump ya karya doka a yunkurin dakatar da biciken da ake yi.