Michael Cohen Zai Ci Gaba Da Bada Shaida A Gaban A Majalisa

Michael Cohen

A yau Laraba ne Michael Cohen, tsohon lauyan Shugaban Amurka Donald Trump, zai koma gaban 'yan kwamitin bincike na majalisar wakilan Amurka don ci gaba da bada shaida.

Wannan kwamitin ya na daya daga cikin kwamitocin da suka kaddamar da binciken gwamnatin shugaba Trump, a karkashin jagorancin ‘yan jam’iyyar Democrats dake majalisar.

Wannan dai shine karo na uku da Cohen yake bayyana a gaban kwamitocin majalisun wakilai da na dattawa a cikin wannan makon, inda yake gabatar da sheda a kan abubuwan da suka shafi Shugaba Trump.

A daya daga cikin shaidar da ya gabatar a kwanan baya, Cohen ya bayyana Trump da cewa maha’inci ne kuma mayaudari, wanda ya umurce shi da ya rufe sirrin danagatakarsa da wasu mata biyu, kuma ya yi karya game da harkokin kasuwancinsa a Rasha.

A jiya Talata ne shugabannin kwamitocin binciken harkokin waje da kuma na gudanarwa suka bukaci fadar White House da ta bada takardun bayanai dake da alaka da duk wata cudanyar da ta gudana tsakanin Trump da Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, inda suka nuna damuwar cewa watakila Trump na boye asiran cudanyar tasu.