A cikin wasikar da suka aikawa sakataren harkokin wajen Amurka, ‘yan majalisar wakilai dake kan Kwamitin Harakokin Waje sunce batun “ya fi karfin China kadai ta magana ce ta kuma yakamata China ta san cewa duniya ba zata kyale ta, tayi abin da ta ga dama ba.”
A cikin amsar da ya bayar, sakataren harkokin wajen na Amurka Mike Pompeo, yace gwamnatin Amurka na tunanin daukar matakan horaswa a kan duk kusoshin gwamnatin China da aka samu suna da hannu wajen gallazawa Musulmin kasar ‘yan jinsin Uighurs.
Amurka dai ta jima tana zargin China da cewa tana cin mutuncin Musulmin dake zaune a sashen arewa-maso-yammacin kasarta, inda take anfani da hujjar cewa tana kokarin magance matsalar ta’addanci ne.
Facebook Forum