Messi Zai Dawo Buga wa PSG Kwallo Bayan Dakatar Da Shi

'Yan wasan PSG suna atisaye (Hoto: AP)

Yayin da ya rage mata wasanni hudu, PSG na saman teburin gasar ta Ligue 1 inda ta ba Lens tazarar maki shida.

Lionel Messi zai dawo bugawa kungiyarsa ta PSG Kwallo a karshen makon nan.

PSG za ta kara da Ajaccio wacce take ta taga-taga a filin wasa na Parc des Princes a ranar Asabar.

Messi bai samu damar buga wa PSG wasanta na baya ba, saboda an dakatar da shi kan kin zuwa atisaye inda ya yi tafiya zuwa Saudiyya ba tare da neman izinin PSG ba.

Bayanai sun yi nuni da cewa ya yi tafiyar ce don gudanar da wani talla a kasar ta Saudiyya.

Yayin da ya rage mata wasanni hudu, PSG na saman teburin gasar ta Ligue 1 inda ta ba Lens tazarar maki shida.