Shahararre dan wasan kungiyar kwallon kafar Barcelona ta kasar Spain Lionel Messi, ya ce zai ci gaba da zama a kungiyarsa ta Barcelona, saboda ba wata kungiya da za ta iya biyan zunzurutun kudaden sayensa da ke kunshe a yarjejeniyar kwantaraginsa. Haka kuma Messi ya ce ba ya fatan ganin ya gurfana a gaban kotu da kungiyar da "ya ke kauna" akan lamarin.
A ranar Talata da ta gabata ne Messi dan kasar Argentina mai shekaru 33, ya aikewa kungiyar wasika ta neman ta ba shi damar yin amfani da dokar da ke kunshe a yarjejeniyar kwantaragin na sa, da ta ba shi damar barin kungiyar a kashin kan sa.
To sai dai shugaban kungiyar ya kafe akan cewa hanya daya da Messi zai iya barin kungiyar shi ne biyan kudin da ke tattare da dokar da adadinsu ya kai yuro miliyan 700, wanda Messi ya ke ganin da wuya a iya samun kungiyar da za ta iya biyansu.
To sai dai a daya bangaren kuma, takwaran Messi a kungiyar ta Barcelona Luis Suarez, zai koma kungiyar Juventus mai fafata gasar Serie A ta kasar Italiya, idan suka cimma daidaito da kungiyoyin 2.
Suarez dan kasar Uruguay na da sauran shekara daya a kwantaraginsa da Barcelona, to amma kungiyar ta fito fili ta nuna cewa baya cikin jerin ‘yan wasan da take bukata, a sabon zubin farfado da ita da suke yi.
Suarez ya koma Barcelonar ne daga Liverpool ta Ingila akan kudi fan miliyan 74 a shekara ta 2014, kuma kawo yanzu ya buga wa kungiyar wasanni 283, inda ya zura mata kwallaye 198.
A jiya Juma’a wasu kafafen yada labaran kasar Italiya sun bayyana cewa Suarez na bukatar yin jarabawar samun zama dan kasa kafin ya sami damar komawa Italiya da taka leda.
Suarez zai rabu da takwaran na sa kuma babban amininsa Lionel Messi, inda zai hade da babban abokin adawarsu Cristiano Ronaldo.