Lionel Messi ya yi bankwana da kungiyarsa ta Barcelona ne cikin hawaye tare da duba yiyuwar komawa PSG da magoya bayansa ke cike da da mammaki.
Kungiyar PSG ta kasar Faransa mamalakin dan asalin kasar Qatar, na ganin Messi dan shekara 34 a duniya a matsayin muhimmin dan kwallo da zai cike mu su gibi a fafutukar samun nasarar su a wasanni musamman a gasar zakarun Turai.
A daren ranar Lahadin, sai da magoya bayan kungiyar PSG suka yi tururuwa zuwa kofar filin tashi da saukar jiragen saman Le Bourget wanda ke arewacin babban birnin kasar ta Faransa wato Paris tare da fatan hango sabon dan wasan da zai cike mu su gibi, saidai ba su sami damar ganinsa ba.
A halin da ake ciki yanzu dai ba’a cimma wata yarjejeniyar fara aiki da PSG da Messi ba saidai a yayin yin jawabin barin kungiyar Barcelona ga manema labarai cikin hawaye, Messi ya ce akwai yiyuwar ya koma PSG da taka leda.
A zahiri dai, kungiyar PSG ce kadai ake ganin zata iya biyan abin da ake tsammanin zai kasance yarjejeniyar da za ta lakume kudi Yuro miliyan 35 a shekara ga Lionel Messi dan asalin kasar Argentina.
A tarihi wasan kwallon kafa dai, ana ganin dan wasa Lionel Messi, ya fi kowanne dan wasa a duniya hazaka, wanda ya shiga kulob din Barcelona tun yana dan shekara 13 a duniya.
Ya kuma ya sami nasarar lashe kofuna 34 a kungiyar Barcelona ciki har da gasar zakarun turai hudu, kofunan La Liga 10 yayin da ya zuwa kwallaye 672 a raga ya kuma kafa tarihi wanda ke cikin dukannin manyan gasannin turai 5.
An dai kai gabar da duk da tayin rage albashinsa da rabi don kulla sabuwar yarjejeniyar shekaru biyar a Barcelona da basussuka na Yuro biliyan 1 da digo 2 kwatankwacin dala biliyan 1 da rabi ke kan ta, kuma dan wasa ya amince da yarjejeniya, sai dai hakan ya sabawa tsauraran takunkumin albashi na League na Sifaniya.
Wasu jiga-jigai a gasar Ligue ta 1 ta Faransa suna ta bayyana mabanbantan ra’ayoyinsu game da zuwan dan wasa Lionel Messi kasar wanda ake ganin zai taka muhimiyar rawa tare da fitaccen dan wasa Kylian Mbappe da Neymar.
A halin da ake ciki, alamun na nuni da cewa kungiyar Barcelona na haramar ci gaba da yin ayyukanta cikin gaggawa duk da barinta da Messi ya yi, inda ta doke kungiyar Juventus sa 3-0 a daren ranar Lahadi a wasan sada zumunta in ji kamfanin dillancin labarai na AFP.
Yunkurin komawar Messi PSG Ya Hadu Da Cikas
Your browser doesn’t support HTML5