Messi Ba Zai Buga Wasan PSG Da RB Leipzig Ba

Lionel Messi

Lionel Messi

Kazalika kungiyar ta PSG ta bayyana cewa Marco Verratti, shi ma bai zai buga wasan ba, saboda yana kan murmurewa daga wata jinya.

Paris Saint-Germain (PSG) ta ce dan wasanta Lionel Messi ba ya cikin jerin ‘yan wasan da za su buga mata wasa da kungiyar RB Leipzig a gasar UEFA.

Cikin wata sanarwa da PSG ta wallafa a shafin yanar gizonta, ta ce, “Leo Messi ya ji ciwo a cinyarsa ta hagu da kuma kwaurinsa.”

A wasan da PSG ta buga da Lille a gasar Ligue 1 a karshen mako, an canza Messi saboda rauni da ya ji.

A kusan karshen wasan kafin a tafi hutun rabin lokaci, an nuna Messi yana dingisawa tare da nuna alamun yana jin zafi.

PSG za ta kara ne da Leipzig ta kasar Jamus a wasannin gasar zakarun turai ta Champions League a ranar Laraba.

Yanzu hakan na nufin sai kocin kungiyar Mauricio Pochettino ya sake lale a ‘yan wasan da za su taka masa leda.

Kazalika kungiyar ta PSG ta bayyana cewa Marco Verratti, shi ma bai zai buga wasan ba, saboda yana kan murmurewa daga wata jinya.

Sai dai rahotanni na cewa Kylian Mbappe, Neymar Jr. da Angel di Maria za su buga wannan wasa.