Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ne ya bayyana haka a wata ganawa da yayi da manema labarai a Abuja.
Ahmed Lawan ya ce majalisar na da tabbacin bangarorin biyu za su warware matsalar da ke tsakanin su.
Ko da yake Majalisar dattawa ba ta yi wata mahawara akan batun kamar yadda majalisar wakilai ta yi ba, duk da cewa an yi ta kiraye kiraye da kakkausar murya cewa majalisar dattawa ta tofa albarkacin bakin ta amma sai ta yi gum da baki.
Da ya ke amsa tambayar manema labarai akan hujjar su na kin yin magana, Shugaban Majalisar Dattawan Ahmed Lawan ya amsa da cewa "an damu mu yi magana batun twitter, to zan yi magana," Yace Ministan watsa Labarai Lai Mohammaed ya riga ya fadi cewa Gwamnatin Kasar na tattaunawa da Kamfanin twitter wajen ganin a shawo kan matsalar, Kuma shi ya yarda da haka.
Bisa ga cewar sa, Twitter tana bukatar Najeriya kamar yadda Najeriya ke bukatar Twitter. saboda haka ya ce baya ga wannan tirka tirkan yana ganin ko wane bangare ya koyi darasi.
To sa idai ga daya cikin masu amfani da dandalin twitter Mohammed Gwani dan London yana ganin ya kamata majalisa ta sa baki saboda su ne wakilan jama'a kuma yan Najeriya miliyan arba'in ne ke amfani da dandalin twitter; Mohammed Gwani ya ce dama 'yan siyasa ne ke ruruta wuta tsakanin Gwamnatin Taraiyya da Twitter in ba haka ba, me zai sa ba za su dauki mataki ba.
Tun ranar 4 ga wana wata da muke ciki na Gwamnatin Najeriya ta bada umurnin rufe dandalin sada zumunta na twitter akan abin da suka bayyana shi a matsayin yi wa shugaba Mohammadu Buhari rashin da'a saboda cire sakon sa da ya wallafa a shafin sa na twitter.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5