Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Takamaiman Lokacin Dage Haramcin Twitter A Najeriya - Gwamnati


Ministan Harkokin Wajan Najeriya, Mr. Geoffrey Onyeama.
Ministan Harkokin Wajan Najeriya, Mr. Geoffrey Onyeama.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa babu wani takamaiman lokaci na janye haramcin da aka yi wa dandalin sada zumunta na Twitter a kasar, har sai ‘yan kasar sun koyi yin amfani da kafar yadda ya kamata.

Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya karbi bakuncin wasu jakadun kasashen waje, da suka hada da Canada, Jamhuriyar Ireland, Burtaniya Amurka da ma tawagar kungiyar tarayyar turai a Najeriya wato EU, wadanda bisa gayyatar ministan suka tattauna akan matakin gwamnatin Najeriyar na dakatar da tuwita a kasar.

Wadannan kasashen na daga cikin na gaba-gaba da suka fito suka soki lamirin gwamnatin Najeriyar akan daukar matakin, ta hanyar fitar da sanarwar da suka rattaba hannun hadin gwiwa game da matakin dakatar da ayyukan dandalin Twitter a Najeriya.

Gwamnatin Najeriyar dai ta ba da sanarwar dakatar da ayukan Twitter a kasar ne, kimanin sa'o'i 48 bayan da kamfanin na Twitter ya shafe wani hoton bidiyon jawabin shugaba Muhammadu Buhai, dangane da yanayin tsaro a kudu maso gabashin kasar.

A yayin wani taron manema labarai jim kadan bayan tattaunawar, Geoffrey Onyeama, ya bayyana cewa dole ne gwamnati ta sauke nauyin da ya rataya a wuyan ta na tabbatar da doka da oda da tsaron rayuka da dukiyoyi.

Ya ce wannan ne dalilin da ya sa gwamnati ta dauki matakin dakatar da ayyukan Twitter a kasar.

Ministan ya ce a halin yanzu dai, babu takamaiman lokacin dage haramcin da aka yi wa dandalin har sai 'yan kasa sun himmatu wajen yin amfani da kafar yadda ya kamata.

Onyeama ya ce gwamnati ba ta ce kafar Twitter na barazana ga Najeriya da kan ta ba, inda ya ce gwamnati ta dauki matakin haramta kafar ne don 'yan kasar su ga mahimmancin amfani da dandalin ta hanyoyin da suka dace, ba kamar yadda wasu tsirarrun mutane da ke neman wargaza zaman lafiya a kasar su ke yi ba.

Haka kuma ya bayyana damuwar gwamnatin Najeriya kan yanayin tabarbarewar tsaro a kasar da kuma matakan da gwamnati ke dauka wajen shawo kan su yana mai cewa, an cimma manufar shirya taron na manema labarai da masu ruwa da tsakin daga kasashen waje.

Onyeama ya kuma ce, gwamnati ta na sane da muhimmiyar rawar da kafofin sada zumunta ke takawa a fanonnin rayuwa daban-daban da kuma yadda kafafen ke da alfanu da matsaloli.

Sai dai ya jaddada cewa matsalolin da ke tattare da yin amfani da kafafen sada zumunta ta hanyoyin da ba su dace ba na mumunan tasiri da kuma barazana ga hadin kan kasa.

Jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary-beth Leonards, a madadin sauran jakadun da suka halarci taron na ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce kasar za ta iya shawo kan matsalolin da ta ke fuskanta komi girmansu, haka kuma duk kasashen na da muradin ganin Najeriya ta ci gaba.

Mary-beth Leonards ta yi wa gwamnatin Najeriya tuni kan muhimmancin samun 'yancin yin amfani da kafafen sada zumunta ba tare da kalubale ba, kana kuma ta yaba da kokarin gwamnati kan tattaunawa da ta ke yi da kafar Twitter don warware takkadamar da ke tsakaninsu

Tuni dai ‘yan Najeriya suka yi ta bayyana mabanbantan ra’ayoyinsu game da matakin na gwamnatin kasar inda wasu ke maraba da shi wasu kuma ke kushewa.

Wasu masana shari’a sun yabawa matakin gwamnatin Najeriya la’akari da yadda kasashen Faransa, Amurka, Burtaniyya da dai sauransu suka yi wa kafar Twitter barazanar dakatar da ayukanta a baya, sakamakon barin wasu yan ta’adda da tsirarrun mutane suna wallafa abubuwan da ka iya tada zaune tsaye.

XS
SM
MD
LG