Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sake Yin Allah Wadai Da Matakin Haramta Twitter A Najeriya


Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken. REUTERS/Jonathan Ernst
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken. REUTERS/Jonathan Ernst

Amurka ta yi Allah wadai da matakin hana amfani da Twitter da hukumomin Najeriya suka dauka tana mai cewa hakan "ba shi da gurbi a tsarin dimokradiyya.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Ned Price ya fada a ranar Alhamis cewa, “‘yancin fadin albarkacin baki da samun bayanai ta hanyar intanet da kuma ta yanar gizo ginshiki ne na ci gaba da kuma tabbatar da zaman lafiyar al’umomin dimokiradiyya.

Ya ce Amurka “ta yi Allah wadai da ci gaba da dakatar da Twitter da gwamnatin Najeriya ta yi da kuma barazanar da za ta biyo baya na kamawa da gurfanar da‘ yan Najeriya masu amfani da Twitter.

Amurka ta damu matuka kan cewar hukumar da ke sa ido kan kafafen watsa labarai ta kasa, ta umarci dukkan masu watsa shirye-shiryen talabijin da rediyo su daina amfani da dandalin na Twitter.

Amurka ta bi sahun Tarayyar Turai, Birtaniyya, Ireland da Canada wadanda a karshen makon da ya gabata suka soki matakin na Najeriya.

Hukumomin Najeriya sun dakatar da Twitter bayan da kamfanin sada zumunta na Amurka ya goge wani sako daga shafin Shugaba Muhammadu Buhari saboda keta dokokinsa.

Sakon na Buhari ya yi magana ne kan yakin basasar kasar shekaru arba’in da suka gabata a cikin wani gargadi game da rikice-rikicen baya-bayan nan, inda yake magana kan “wadanda ke nuna rashin da’a” a tashin hankali a yankin kudu maso gabashin kasar.

Jami'ai a can suna zargin haramtacciyar kungiyar 'yan awaren IPOB da kai hare-hare kan 'yan sanda da ofisoshin zabe.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG