Kamfanin Facebook ya bayyana da kudirin sa na daukar hayar sababbin ma’aikata, da suka hada da malaman jami’a, a wani kokarin kyautata manhajojin sa da kuma inganta kamfanin don dai-daito da zamani.
Kamfanin yayi la’akari da yadda duniya ke samun cigaba musamman idan aka yi duba da yadda na’urorin zamani ke juya duniya, na’urar mutunmutumi na daya daga cikin hanyoyin dake kawo sauyi a duniya.
Kamfanin ya dauki hayar wata sananniyar malama wadda tayi fice a fannin sarrafa na’urar zamani da ta shafi amfani da mutunmutumi, za’a iya amfani da na’urar robot a cibiyoyin ajiyar na’urorin kamfanin.
Sabon tsarin zai taimaka wajen ajiye bayanai cikin inganci, kana da samar da tsari da duk wata na’ura zata iya dauko labarai cikin sauki ba tare da bata lokaciba.
Amfani da robot zai taimaka wajen gane yadda mutane ke koyan karatu da sauran abubuwan yau da kullun, ta haka kamfani zai iya kyautata dangantakar sa da abokan hurda.