Babbar kotun tarayya a jihar California ta Amurka ta yanke ma tsohon injiniya ma’aikacin kamfanin Apple hukunci, biyo bayan tuhumar sa da aka yi da satar bayanan sirri na kasuwancin da suka shafi mota mai tuka kanta, wanda yake yunkurin barin kasar don neman mafaka a kasar China.
Jami’an tsaron karamar hukumar San Jose a jihar ta California sun kama Xiaolang Zhang a ranar Asabar, jim kadan kafin tashin jirgin sa na barin kasar.
Injiniyan da ya dauki hutu don taya mai dakin sa renon jaririyar da aka haifa misa, bayan dawowar sa daga hutu ya bayyana ma shugaban kamfanin cewar zai bar aiki a kamfanin, biyo bayan aiki da ya samu a kamfanin Xiaopeng Motors na kasar China.
Kamfanin dai na kokarin kera mota mai tuka kanta, amma kyamara ta dauki hoton bidiyon injiniyan yana shiga dakin ajiye bayanan sirri na mota mai tuka kanta na kamfanin Apple inda ya nadi bayanan sirri a kwamfutar sa a dai-dai lokacin da yakamata ace yana kasar China.
Facebook Forum