Me Jam’iyyar PDP Ke Ciki Bayan Hukuncin Kotu?

PDP

Biyo bayan kwashe shekaru ana takaddamar shugabancin jam'iyyar PDP, wanda yanzu haka kotu ta tabbatar da Ahmed Makarfi a matsayin shugaban jam'iyyar.

Hukuncin da kotun koli ta yanke na mika shugabancin jam’iyyar PDP ga bangaren Ahmed Makarfi, ya bude sabon babi a jam’iyyar da ka iya kawo sararawa bayan zulumin jam’iyyar tun faduwa zabe a shekarar 2015.

Ga Shugaban Kwamitin amintattun jam’iyyar Sanata Walid Jibrin, wanda bai taba raba tunanin jam’iyyar ta bangaren mafiya rinjaye zai sami nasara.

Walid Jibrin, ya ce abin da ke fitowa daga jam’iyyar PDP yanzu haka na zuwa ne sakamakon karfin da kungiyar ke da ita da kuma yawan jama’ar jam’iyyar.

Sakataren shirye-shirye na kwamitin rikon PDP, Abdul Ningi, ya ce sun huta da rigima domin daman can suna da yakinin ba zasu taba daidaitawa ba da Sanata Sherif ta taiburin shawara ba.

A tsarin PDP na kwamitin riko da aka karawa wa’adi na shekara ‘daya wajen karshen wannan shekarar kenan, zai shirye sabon zaben jam’iyya da zabar shugaba daga bangaren kudu inda dan takarar shugaban kasa ga zaben 2019 ya koma arewa.

Cikin masu niyyar takara daga PDP kai tsaye ko ta bangaren mukarrabansu akwai tsohon gwamnnan Jigawa, Sule Lamido da kuma kwanannan mukarraban gwamnan Gombe Ibrahim Hassan Dan Kwanbo suka ce zasu nemeshi yayi takarar shugabancin.

Yanzu haka dai PDP ta fita daga batun takaddamar shugabancin jam’iyya inda take ganin zata iya dawowa mulkin Najeriya a shekarar 2019.

Your browser doesn’t support HTML5

Me Jam’iyyar PDP Ke Ciki Bayan Kotu Ta Tabbatar Da Shugabanta? - 3'00"