Me Buhari Yake Ciki a Taron G7?

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da Angela Markel shugabar gwamnatin Jamus.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da Angela Markel shugabar gwamnatin Jamus.

Litinin dinnan itace ranar karshe da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake hallartar taron kasashen duniya wadanda suka fi karfin tattalin arziki ko G7.

Ko me shugaban yake ciki a halin yanzu? Mallam Garba Shehu shine kakakin Buhari wanda yanzu haka yake tare da shi a birnin Munich na kasar Jamus.

“Shugaba Buhari kamar tauraro ne a cikin shuwagabannin, wannan ya ja shi nan, wannan ya ja shi can. Idan an fito (tattaunawa) da wannan shugaban kasa, a yi da wannan. Zuwa yanzu wasu ma sun hakura basu samu yin magana da shi ba, sunyi sallama sun tafi.”

A dai-dai wannan lokaci da Sashen Hausa na Muryar Amurka yake rubuta wannan labarin, Buhari yana tattaunawa da shuwgabannin kasashen duniya.

Ko me za’a tattauna game da Najeriya a taron na G7?

Mallam Garba yace “na farko dai, kowa ya san halin da kasar ta mu take ciki. Matsalar tsaron nan, da ake ta fama da ita, wadda yake su kansu sauran shuwagabanni sun san da ita. Itace yake ta kokari ya samu hadin kai na kasashe. An fara da makota, yanzu gashi muna nan, maganar nan ana ta yinta”

“Akwai kuma matsaloli na harkar tattalin arziki da ma kawo cigaba a Najeriya. Harkar ilimi, da harkar wutar lantarki, harkar rashawa da cin hanci, muhimman abubuwa dai da shi Shugaba Muhammadu Buhari ya saka a gaba. Muna kyautata zato, kuma za’a samu cigaba da goyon baya na wadannan kasashe” a cewar Garba Shehu.

Tun bayan hawa karagar shugbanci, Muhammadu Buhari ya tafi kasashen Nijar da Chadi akan batutuwa na tsaro, sannan a halin yanzu yana Jamus domin tattaunawa da shuwgabannin kasashen duniya wadanda suka fi karfin tattalin arziki.

Your browser doesn’t support HTML5

Me Buhari Yake Ciki a Taron G7? – 6’07”

Shugaba Buhari a Taron G7