MDD Ta Hada Gwiwa Da Matasa Don Yaki Da Cin Hanci A Nijar

Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana

A yayinda ake bikin tunawa da ranar yaki da cin hanci ta duniya a yau 9 ga watan Disamba kungiyar Transparency International reshen Nijar ta bayyana damuwa game da abin da ta kira tarnakin da ake fuskanta a wannan gwagwarmaya sakamakon wasu dalilan da ke da nasaba da raunin doka

A bana MDD ta bayyana bukatar hada gwiwa da matasa a yaki da cin hanci ta yadda za a sami wanzuwar dabi’ar kare mutuncin kai a gaba.

Tun daga shekarar 2003 da aka kaddamar da yarjejeniyar yaki da cin hanci ta MDD ranar 9 ga watan Disamban kowace shekara ke zama wani lokacin bitar halin da ake ciki a kowace kasa a wannan yaki da nufin zakulo sabbin hanyoyin da za a bullo wa al’amarin mai bijiro da sabbin kamani a kulayomi.

Da yake bayyana halin da ake ciki a wannan fanni a Nijar, kasar da hukumomin mulkin soja suka kudiri aniyar murkushe cin hanci da rashawa, Shugaban Transparency International, Maman Wada, na cewa yunkurin na fama da kwan-gaba kwan-baya.

Mamba a kungiyar farar hula ta M62, Falamata Taya, wace ta jaddada kyaukyawar aniyar hukumomin kolin kasar game da yaki da cin hanci, na zargin wasu mukarrabai da yi wa yunkurin zagon kasa.

Kamarin cin hanci a harkokin jama’a a yau wanda kuma ke zama wata matsala mai wuyar magancewa cikin kankanin lokaci ya sa MDD a bana ta karkatar da hankali wajen matasa don ganin watan wata rana an wayi gari da wata al’ummar da ta fahimci illolin cin hanci ta kuma guji abin.

Rahotn kungiyar transparency na 2023 ya saka Nijar a matsayin kasa ta 125 a sahun kasashe 180 abin da ke fayyace girman matsalar cin hanci a kasar wace a baya ake ayyana dalilan siyasa da katsalandan na shugabanni a matsayin abubuwan da ke hana ruwa gudu a yaki da wannan mummunar dabi’a.

Saurari cikakken rahoto dagaSouley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Yayin Da Ake Bikin Ranar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa, Nijar Na Tsakiyar Matsalar