Kasashen Afirka a Kwamitin Sulhun MDD, jiya Alhamis sun yi maraba da rattaba hannu na dindindin da aka yi tsakanin Shugaban Sudan Ta Kudu da tsohon Mataimakinsa, to amma sun bayyana damuwar cewa, kamar sauran yarjajjeniyoyi na baya, wannan ma ba za ta dore ba.
Shugaba Salva Kiir da mai ja da shi kuma tsohon Mataimakinsa, Riek Machar, sun rattaba hannu kan yarjajjeniyar ranar Talata a Khartoum.
Jakadan Sudan Ta Kudu a MDD, Akuei Bona Malwa, ya ce wannan yarjajjeniyar ta hada da sauran bangarorin da ke taka rawa a wannan tashin hankalin, kuma dukkanninsu sun yi alkawarin hada kai wajen maido da zaman lafiya a kasar.
Jakadan Habasha Tekeda Alemu ya ce kwanakin da ke tafe za su kasance da matukar muhimmnaci.
Ya kara da cewa:
"Abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne, kamar yadda aka sani, dukkannin bangarorin su mutunta alkawarin da su ka yi su aiwatar da zaman lafiya."
Shi ma jami'in diflomasiyyar kasar Ivory Cost ya yi kira ga dukkannin bangarorin da su mutunta alkawarin da su ka yi, ya kuma ce gwamnatin kasarsa ta amince da girke sojojin hadin gwiwa na kungiyar kasashen Kuryar Afirka, domin tabbatar ana mutunta ka’idodin yarjejeniyar tsagaita bude wutar.