Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sudan ta Kudu da 'Yan Tawaye Sun Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta


Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar sun sha hannu bayan sun rabtaba hannu akan yarjejeniyar tsagaita wuta
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar sun sha hannu bayan sun rabtaba hannu akan yarjejeniyar tsagaita wuta

Biyo bayan taron da gwamnatin Habasha ta shirya tsakanin shugaban Sudan ta Kudu da madugun 'yan tawaye wanda ya samu halartar shugaban Sudan Bashir, abokan gaban sun cimma matsaya sun kuma rabtaba hannu akan yarjejeniyar tsagaita wuta da zata fara aiki sa'o'i 72 daga lokacin da suka sa hannu

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugun ‘yan tawayen Riek Machar, sun rattaba hannun kan wata yarejejeniya tsagaita wuta ta dindindin a daukacin kasar, wacce aka kulla a Khartoum, babban birnin Sudan a jiya Laraba.

Shirin tsagaita wutan, Zai fara aiki ne cikin sa’o’i 72 daga lokacin da aka rattaba hannun.

Wannan matsaya da aka cimma, ta hada har da wani tsari da zai samar da tsaro ga filayen da ake hakar man fetur a kasar tare da bunkasa ababan more rayuwa.

Sai dai matsayar ba ta hada har da batutuwan da aka jima ana takaddama akansu ba, kamar na yadda za a raba mukamai da kafa gwamnatin hadaka da kuma makomar dakarun ‘yan adawa.

Ita dai wannan yarjejeniya, wacce ta ayyana dakatar da kai duk wasu hare-hare a mataki na dindindin a Sudan ta kudu, za a gina ta ne akan matsayar da aka cimma ta tsagaita wuta a watan Disambar bara a tsakanin wakilan Kiir da Machar da kuma jam’iyyun siyasar kasar.

Yayin da yake jawabi a wajen bikin kulla wannan yarjejeniya, Machar wanda a da shi ne tsohon mataimakin shugaban kasar, ya ce “wannan matsaya da aka cimma tana da ma’ana, za ta kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake samu, na yi imanin cewa al’umar Sudan ta Kudu za su kasance masu cike da farin ciki, domin za a tsagaita wuta nan da kwanaki uku.”

Yayin jawabinsa, Kiir, ya fara jinjina ma shugaban Sudan Omar Al Bashir ne, wanda ya shirya wannan zama na gaba-da-gaba, da ya kai ga cimma wannan matsaya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG