Har yanzu, kungiyar Paris Saint-Germain ta kasar Faransa, ta yi gum da tayin da Real Madrid ta yi na sayen dan wasanta Kylian Mbappe.
A tayin da ta yi na biyu, Madrid ta ce za ta sayi Mbappe akan kudi euro miliyan 154.4.
Sai dai PSG wacce take ta kokarin shawo kan Mbappe ya sabunta kwantiraginsa, ta ki amsa tayin ko ta yi watsi da shi.
A watan Janairun badi kwantiragin Mbappe zai kare a kungiyar ta PSG.
Hakan nufin mai yiwuwa Real Madrid sai ta jira har sai karewar kwantiragin nasa kafin ta samu dama daukan dan wasan mai shekara 22.
A ranar Litinin Mbappe dan asalin kasar ta Faransa, ya fadawa kungiyar ta sa ta PSG cewa shi fa Real Madrid ya nufa.
A ranar Lahadi Mbappe ya ci wa PSG kwallaye biyu a karawar da ta yi da Reims wacce suka doke da ci 2-0.
A wasan na ranar Lahadi Lionel Messi wanda PSG ta yi cefanensa daga Barcelona makonnin uku da suka gabata, ya fara bugawa kungiyar kwallo.