Sabon dan wasan Chelsea Rumelu Lukaka da ya yi kome, ya zura kwallonsa ta farko a kungiyar ta ‘Blues’ a karawar da suka yi da Arsenal a gasar Premier ta Ingila.
Chelsea ta doke Arsenal da ci 2-0 a wannan karawa wacce aka buga a filin wasa na Emirates a ranar Lahadi.
Dan shekara 28, Lukaku ya zura kwallonsa ne a minti na 15 da fara wasa, sannan Reece James ya biyo da kwallo ta biyu a minti na 35.
Arsenal ta samu damar fenariti a lokacin da aka kada Bukayo Saka amma alkalin wasa bai amince ba.
Kungiyar ta sayo Lukaku akan kudi fam miliyan 97.5, wannan kuma shi ne karo na biyu yake zuwa ya bugawa kungiyar wasa daga Inter Milan wacce ta saye shi a 2019.
Dan asalin kasar Belgium, Lukaku shi ne dan wasa kwallon kafa na bakwai cikin jerin ‘yan wasan da aka yi cefanan su.