MINNA, NAJERIYA - Al'ummomin dai sunce har yanzu basu koma cikin hayyacinsu ba asakamakon wannan Mummunan kisa na kare dangi da yanbindigar sukayi a wannan gari.
A lokacin da Mataimakin Gwamnan jihar Nejan Alhaji Yakubu Garba ya ziyarci garin na Madaka sun bukaci Gwamnatin Nigeria da ta kara tura karin jami'an tsaro a wannan yanki.
Yankin na Madaka dai yana fama da matsalar rashin hanyar mota duk da kasancewar yankin ya shahara wajan aikin noma.
A ranar laraban makon jiya ne maharan dauke da manyan bindigogi akan babura suka auka babbar kasuwar garin da misalin karfe uku na rana inda bsude wuta tare bankawa kasuwar wuta.
Har zuwa wannan lokaci ba asan inda kimanin mutane 25 suke ba.
Mataimakun Gwamnan jihar Nejan Alh. Yakubu Garba yace yaje garin ne domin yin jaje akan wannan bala'i da ya samesu, sannan ya bada tabbacin tura karin jami'an tsaro a wannan yanki.
Yankin na Madaka dai ya dade yana shan ukubar wadan nan yan ta'adda domin kuwa ko a cikin shekarar bara ma 'yan bindigar sun hallaka Babban basaraken garin tare da yin garkuwa da wasu da dama.
A saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5