Mayakan Kurdawa Sun Kara Samun Nasara Kan Mayakan IS

Mayakan Kurdawa

Mayakan Kurdawa da ake kira “Peshmerga” dake samun taimakon sojan atilere na kasar Turkiya, a jiya Lahadi sun kara samun nasara a kan mayakan IS dake wajen Mosul, birni mafi girma na biyu a kasar Iraqi, har ma a wani lokaci suka ce suna dab da garin Bashiqa.

Komandodin mayakan Kurdawan sun shaidawa manema labarai a wajen garin na Bashiqa cewar mayakan nasu sun shiga cikin garin Bashiqa din mai tazaran kilomita goma arewa maso gabashin bangaren Mosul da mayakan IS suka.

Da yake an hana ‘yan jarida shiga garin, ba tabbas na halin da yake ciki har zuwa safiyar yau Litini.

YDuk wannan al’amarin dai yana faruwa ne daidai akin lokacin da sakataren tsaron Amurka Ash Carter yake ziyaraa kasar, inda yake tattauanwa da shugaban Kurdawa Masoud Barzani da manyan hafsoshin sojinsa a garin Irbil dake kusa da Mosul din.

Carter wanda ya gana da shugaba Racep Tayyib Erdowan na kasar Turkiya a ranar Juma’a, yana neman kwantar da tarzoman dake tsakanin shugabannin Sunni na Turkiya da kuma gwamnatin Shi’a ta Iraqi ne, wadanda ke ta cece-kuce da juna sakamakon mayaka dubu daya da Turkiya ta jibgesu a kusa da Bashiqa a karshen waccan shekara don su horar da yan Sunni da Kurdawa dake yaki da dakarun kungiyar IS.