Mai Magana da yawun ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD, Jens Laerke yace “ Abin takaici baza a iya kwashe marasa lafiya da wadanda suka ji rauni a safiyar yau kamar yadda aka shirya ba, a saboda har yanzu ba’a samar da yanayin da ake bukata na yin hakan ba."
Laerke bai bayyana bangarorin da suka kasa cika alkawuran tsagaita wuta don ayyukan jinkai kamar yadda Rasha ta bayarda umurni kwana guda kafin nan ba. To sai dai kawai yace Majalisar Dinkin Duniya da al'ummar Aleppo suna cikin wani mawuyacin hali mai tsanani.
A jiya Alhamis ne Rasha taba da umarnin kara tsawon wa'adin aiki da shirin tsagaita wuta na jinkai a Aleppo da awa 24.
Shirin tsagaita wutar farko inda Syria da Rasha suka daka tar da hare hare ta sararin samaniya a ranar Talata a Aleppo, an shirya karewarshi ne jiya Alhamis da karfge 7 na maraice agogon kasar kafin a kara tsawon wa'adinsa.