Mayakan Jihadi Sun Kashe Jami'an Tsaro Sama Da 50 A Burkina Faso

Mayakan jihadi

Sama da jami'an tsaro 50 ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a wani kazamin fada da masu jihadi a arewacin Burkina Faso, in ji rundunar sojin kasar a jiya Talata.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, an kashe sojoji 17 da mayakan sa-kai guda goma sha takwas, wadanda ke taimakawa sojoji a yankin Koumbri da ke lardin Yatenga a ranar Litinin. Hakazalika an kashe da dama daga cikin mayakan na IS, a wani mataki na kokarin fatattakar mayakan daga Koumbri domin mutanen da suka rasa matsugunansu su koma, in ji rundunar.

“Wannan aikin na ‘yan matsorata ba za mu fasa hukunta su ba. Ana duk iya kokari don ganin an murkushe sauran ‘yan ta’adda da suka gudu,” in ji sanarwar.

Al'ummar yammacin Afirka dai na fama da hare-haren ‘yan jihadi da ke da alaka da al-Qaida da kuma kungiyar IS da suka yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da raba sama da mutane miliyan 2 da muhallansu da kuma jefa dubun-dubatar cikin halin yunwa. Rikicin dai ya raba kasar da a da ta ke cikin zaman lafiya, sai ga shi ya kai ga juyin mulki sau biyu a shekarar da ta gabata da kuma kara kai hare-hare, da ke kewaye da babban birnin kasar, Ouagadougou.

Tun bayan juyin mulkin farko a watan Janairun 2022 adadin mutanen da mayakan jihadi suka kashe ya kusan ninka sau uku idan aka kwatanta da watanni 18 da suka gabata, a cewar wani rahoto da cibiyar nazarin dabarun Afirka ta fitar.

Kisan na ranar litinin na daya daga cikin hare-hare mafi girma tun bayan da Kaftin Ibrahim Traore ya kwace mulki a juyin mulki na biyu a watan Satumba, kuma ya sabawa daya daga cikin manyan dakarun soji, in ji Rida Lyammouri, babban jami'a a Cibiyar Siyasa ta New South, da ke Morocco.

Kungiyoyin kare hakki da manazarta sun zargi jami'an tsaron da kashe fararen hula da ake kyautata zaton suna da alaka da masu jihadi.

Cibiyar nazarin dabarun Afirka ta ce adadin fararen hula ma’aikatan sa kai da sojoji suka kashe tun bayan juyin mulkin farko ya ninka fiye da sau uku zuwa 762 idan aka kwatanta da shekara da rabi da ta gabata.

A wani bincike da ya gudanar a farkon wannan shekarar, Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya gano cewa jami'an tsaron Burkina Faso sun kashe kananan yara a wani sansanin soji da ke wajen garin Ouahigouya.

~ AP