Mayakan Boko Haram suna shawagi a wasu kauyukan karamar hukumar Madagali dake kusa da dajin Sambisa inda har yanzu mayakan ke da karfi.
Da safiyar yau 'yan Boko Haram suka sake kai hari a wani kauyen da ake kira Wanu, inda suka yi kashe-kashen rayuka da kone-kone.
Wani mazaunin yankin da baya son a ambaci sunansa ya ce ilahirin al'ummar Madagali, na cikin zaman dar-dar, duk da cewa akwai jami'an tsaro amma bai hana 'yan Boko Haram ci gaba da kai hari ba saboda jami'an tsaron wuri daya su ke suna tsaron kansu, inji shi. Mazauna yankin yanzu basa iya barci.
Dan Majalisar Wakilai dake wakiltar yankin Mr. Adamu Kamale, ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da cewa yau ma sun tashi da bakin ciki saboda kisan mutane da aka yi tare da kone gidaje da dama. Ya ce har yanzu mutanen, wato, 'yan Boko Haram, ba su yi nisa dasu ba. A cewarsa jami'an tsaro sun kasa.
Shi ma shugaban karamar hukumar Madagalin Yusuf Muhammad, cewa ya yi idan ba'a kai masu dauki cikin gaggawa ba akwai yiwuwar wasu al'ummar yankin zasu gudu zuwa kasar Kamaru. Bukatarsu yanzu ta tsaro ce, injishi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5