Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Ci Gaba Da Kwaso ‘Yan Najeriya Daga Libya - Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Daga dama) Firai Ministan Italiya Matteo Renzi (Daga hagu) yayin da ya kai ziyara Najeriya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Daga dama) Firai Ministan Italiya Matteo Renzi (Daga hagu) yayin da ya kai ziyara Najeriya

Yayin da a sassan duniya ake ci gaba da Allah wadai da zargin cewa ana sayar da bayi a Libya, taron koli na hadin gwiwa tsakanin kungiyar tarayyar Afirka da takwarar aikinta ta EU da ke gudana a Cote d' Ivoire, ya maida hankali kan yadda za a yi amfani da matasa wajen samar da ci gaba mai dorewa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da maido da ‘yan Najeriya da ke gararamba a Libya idan har aka gane su, kamar yadda wasu jaridun Najeriya suka ruwaito.

Bayanin na Buhari na zuwa ne yayin da rahotanni ke nuna cewa an bude wata kasuwar sayar da bayi ta bakaken fata a kasar inda akan ci zarafinsu.

Shugaba Buhari ya yi wadannan kalaman ne yayin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya mazauna Cote d’ Ivoire a gefen taron koli na hadin gwiwa tsakanin kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta AU da takwarar aikinta ta EU da ke wakana a Abdijan, babban Birnin Cote d’ Ivoire.

Buhari ya kara da cewa za a samar da wani shiri da zai rika warkar da zukatan ‘yan Najeriya masu kwadayin zuwa nahiyar turai domin neman sabuwar rayuwa.

Wannan taro na koli wanda ke gudana a karo na biyar ana gudanar da shi ne tsakanin ranakun 29-30 a wannan wata na Nuwamba.

Taken taron shi ne “yadda za a yi amfani da matasa wajen samar da ci gaba mai dorewa.”

Yayin jawabin nasa, Buhari ya ce ta iya yiwuwa ‘yan matan 26 da suka mutu akan teku a kwanakin baya duk ‘yan Najeriya ne, kamar yadda jaridar ta Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa, babu mamaki ikrarin da ake yi na cewa ‘yan Najeriya uku ne kacal cikin ‘yan matan, adadin ya fi haka.

A makon da ya gabata hukumomin Italiya suka yi jana’izar ‘yan mata bakin haure 26 da aka tisnci gawarwakinsu akan teku.

Jaridar ta Daily Trust da ake wallafawa a Abuja, ta ruwaito mai bai wa shugaban shawara kan ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri na cewa an kwashe akalla ‘yan Najeriya 5,000 daga kasar ta Libya.

Sai dai Dabiri ta ce abin alhinin shi ne duk da haka wasunsu na kara komawa kasar ta Libya.

A kwanakin da suka gabata ne, kafar talbijin ta CNN da ke Amurka ta watsa wani rahoto na musamman da ya nuna yadda aka gano wata kasuwar sayar da bayi bakaken fata ‘yan Afirka.

Lamarin da ya ja hankulan kasashen duniya tare da gudanar zanga zanga nuna kyamar lamarin.

Gidan talbijin na CNN ya ruwaito cewa ana sayar da kowane mutum guda akan farashin dala 400.

Sai dai masu fada a ji a kasar ta Libya sun musanta wannan zargi na kasancewar wata kasuwar sayar da bayi.

Libya ta kasance cikin rudani siyasa tun bayan da aka hambarar da gwamnatin Moammar Ghaddafi a watan Oktoban shekarar 2011.

Hakan kuma ya haifar da kungiyoyi masu dauke da makamai daban-daban da ke ikrarin mallakar ikon kasar.

Ita dai Libya kasa ce da ta zamanto mahada ko kuma kofa da bakin haure ke samun damar ketarawa zuwa nahiyar turai.

Wannan lamari ya sa matasa, maza da mata a wasu lokuta ma har da yara daga sassan Afirka suke tururuwar zuwa kasar domin ketarawa zuwa nahiyar ta turai.

Saurari rahoton da wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El Hikaya ya hada kan taron kolin na AU da EU:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG