Mawakin Gambara DMX Ya Mutu 

DMX

Iyalan mawakin salon wakar gambara ko kuma rap, DMX, sun ce mawakin ya rasu. 

DMX wanda ya fito idon duniya da wakarsa ta “Ruff Ryders Anthem” ya rasu yana da shekara 50.

Wata sanarwa da iyalansa suka fitar ta ce, DMX, wanda an taba saka sunansa cikin jerin sunayen wadanda za a zaba domin lashe lambar yabo ta Grammy, ya rasu ne a asitibin White Plains a New York da ke Amurka.

DMX/AP

“Ya rasu da iyalansa a gefensa, bayan da aka saka shi akan na’urar tallafawa numfashi a cikin kwanakin da suka gabata.” Kamfanin dillancin labarai na AP ruwaito.

A ranar 2 ga watan Afrilu aka garzaya da DMX asibiti a birnin na New York. Asibitin ya ce yana fama ne da “matsalar bugun zuciya.”

DMX/AP

Shi dai DMX wanda asalin sunan Earl Simmons, na daya daga cikin mawakan da suka fito da wani irin salon wakar gambara, ya kuma shahara har ila yau a fitowa a fina-finai.

Sai dai daga baya ya sha fama da shara’o’i a kotu da matsalar shan miyagun kwayoyi - al’amuran da suka disar da tauraronsa.