Tsohon dan Majalisar Wakilan Amurka Matt Gaetz ya janye sunansa daga jerin wadanda zababben Shugaba Donald Trump zai zaba a matsayin antoni janar a yau Alhamis.
washington dc —
Gaetz yace batun tantance shi ya fara daukar hankula.
"Babu batun bata lokaci a kan wata turka-turkar siyasar birnin Washington maras fa'ida, don haka na janye sunana daga jerin wadanda za'a zaba a matsayin antoni janar," kamar yadda Gaetz, dan jam'iyyar Republican ya wallafa sako a shafinsa na X.
"Wajibi ne ma'aikatar shari'ar ta zama cikin shiri tun a ranar farko"
Sanarwar na zuwa ne kwana guda bayan da Kwamitin Da'ar Majalisar Wakilan ya shiga dambarwa bayan sakin wani rahoto game da zargin aikata lalata da ta'ammali da miyagun kwayoyi a kan Gaetz kuma bayan da ya gana da sanatocin jam'iyyar Republican din zai bukaci gudunmowarsu domin zama antoni janar.