Kingsley Moghalu ya bayyana cewa baya ganin laifin matasan Najeriya da ke barin kasar don zuwa wasu kasashen duniya da suka ci gaba don samawa kan su ci gaba na rayuwa.
A yayin da yake magana a wani shirin tattaunawa wato 'The Chat' na gidan talabijin na Channels a radar Lahadi, Moghalu ya jadada cewa halin da tattalin arzikin kasar ke ciki abin takaici ne kuma hakan ya ke karyawa matasa gwiwa wajen ci gaba da jure yanayin da ba sa ganin mafita a kai.
A cewar Moghalu, ya kamata gwamnatoci a duk matakai su bullo da sabbin dabaru da daukar matakan da suka dace don farfado da tattalin arzikin kasar.
Ya ce bashi da karfin gwiwa kan shugabannin Najeriya saboda yadda ba su cika yin gaskiya ba, inda ya ce da zai iya shiga daya daga cikin manyan jam’iyyun siyasar kasar biyu wato APC da PDP a shekarar 2019 amma a mu’amalarsa da yan siyasar ya fahimci cewa babu daya daga cikin jam’iyyun 2 da zata iya taimakawa wajen kawo sauye-sauye masu amfani ga kasar.
Kazalika Moghalu ya ce a shekarar 2019 ya sami damar shiga jam’iyyar PDP ko APC amma ya shawarci kansa kan cewa gwara ya gabatar da kudurorinsa na siyasar hangen nesa ga‘ yan Najeriya.
Moghalu wanda fitaccem lauya ne kuma masanin tattalin arziki, shine tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar Jam'iyyar Young Progressives Party wato YPP a zazen shugaban kasa na shekarar 2019, wanda ya bar jam’iyyarsa ta YPP a watan Oktoban shekarar 2019 kuma a cikin kwanan nan ya shiga jam’iyyar ADC.
Idan ana iya tunawa, jam’iyyar ADC ta tsayar da fitaccen masanin tattalin arziki da harkokin gudanarwa, Patrick Okedinach Utomi wanda aka fi sani da Farfesa Pat Utomi a matsayin dan takarar shugaban kasarta a zaben shekarar 2007.