Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Ci gaba Da Taimakawa Najeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci – Amurka


Shugaban Amurka, Joe Biden
Shugaban Amurka, Joe Biden

Blinken ya kara da cewa, Amurka na jinjinawa Najeriya kan irin jagorancin da take yi a nahiyar Afirka wajen samar da zaman lafiya da tsaro.

Gwamnatin Amurka ta bayyana shirinta na ci gaba da tallafawa Najeriya a fannoni da dama ciki har da batun matsalar tsaro musamman yaki da ayyukan ta’adanci.

Cikin watan sanarawa da Sakataren harkokin wajen Amurka Antony J. Blinken ya fitar don taya Najeriya cika shekara 61 da samun ‘yancin kai, Blinken ya ce baya ga fannin tsaro, Amurka za ta kuma ci gaba da tallafawa kasar a fannonin kiwon lafiya, bunkasa tsarin dimokradiyya da tattalin arziki.

“A madadin Gwamnatin Amurka da al’umarta, Ina mika fatan alheri ga al’umar Najeriya yayin da take bikin cika shekara 61 da samun ‘yanci.” Sakatare Blinken ya fada a cikin sanarwar.

Ya kara da cewa, “kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashenmu biyu ta dogaro ne kan manufofin iri daya da muka sa a gaba ta fuskar bin tsarin dimokradiyya da kuma fuskar kasuwanci.”

Blinken ya kara da cewa, Amurka na jinjinawa Najeriya kan irin jagorancin da take yi a nahiyar Afirka wajen samar da zaman lafiya da tsaro, kawo karshen annobar COVID-19 da samar da kwakkwaran tattalin arziki da rage hanyoyin gurbata muhalla da samar da tsaftatattun hanyoyi.

“Amurka na muradin ganin mun kara yaukin dangantakarmu cikin shekaru masu zuwa tare da kare abubuwan da muka sa a gaba.”

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG