“Muna so mu jaddada matsayi uku wadda muka dauka, tun wannan lokaci, har zuwa yanzu”, inji Farfesa Ango Abdullahi.
“Matsayi na farko shine, dole, dole ayi zabe na wannan shekara 2015 irin yadda tsarin mulki ya ajje. A baiwa jama’ar kasa dama su zabi shugabanninsu.”
“Matsayi na biyu shine har yanzu tsarin mulki ya ce ranar 29 ga watan biyar, na wannan shekara (2015), dole a samu gwamnatoci sababbi, a kasa baki guda, da jihohi ranar 29 a sakamakon, ina kara karfafa wanna, a sakamakon zabe wanda za’a yi, a tabbatar da cewa wadannan sababbin gwamnatoci da za’a yi a kasa da Jihohi, za’a yi su da yawun mutanen da suka zabe su.”
“Na uku, mun tsaya akan cewa baza mu taba yadda, da wata gwamnati wadda ba zababbiyar gwamnati bace, a wannan shekarar” a cewar Mr. Abdullahi.
Farfesa Ango Abdullahi bai bayyana matakan da kungiyar zata dauka ba, idan aka karya wannan matsayi da kungiyar da yake wakilta ta dauka.
Kura ta turnuke, tun bayan dage babban zaben kasa baki daya a Najeriya, wanda yanzu haka ake shirin yinsa ran 28 ga watan Maris.
Your browser doesn’t support HTML5