A yau Alhamis ne dai ‘dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya ta APC Janal Muhammadu Buhari, zaiyi jawabi a cibiyar manufofin harkokin kasashen waje da ake cewa Chatam House, da turanci a birnin London. Ana sa ran zai tattauna da wasu kososhin siyasar Birtaniya, kuma zai hadu da masu ruwa da tsaki wadanda ke da sha’awa kan siyasar Najeriya.
Kan wannan tafiyar ta Buhari ce dai Aliyu Mustapha, ya tuntubi mai baiwa shugaba Goodluck Jonatha shawara kan harkokin siyasa Farfesa Rufa’I Ahmed Alkali, don jin ra’ayin jam’iyyar PDP game wannan tafiya da Buhari yayi da kuma haduwa da shugabannin siyasar turai da yake.
Farfesa Rufa’I yace, “wannan ba laifi bane ai tunda yake duk wanda zai shugabanci Najeriya, yakamata ya zama shugaban kasa ne wanda kuma dole ne yana da mutunci a idon duniya.” Ya dai ce basu da wata damuwa game da cudanyar da shi Janal Buhari, yake da shugabannin turai, kasancewer shima shugaban kasa dake kan mulki Goodluck Jonathan, yana ire-iren wannan zagaya duniya.
Kuma duk wani mutum da yake neman siyasa babu inda baya zagayawa domin neman jama’a, kuma ra’ayi na kasashen waje nada muhimmamci ga ‘dan takara, daga karshe dai zabe a kasar Najeriya za’a dawo ayi.