Wannan matsalar matsanancin zafin ya sa jama’a kwana a waje, su kuwa hukumomin kiwon lafiya na gargadin a kula.
Ciki zafi – waje – zafi halin da al’umman jihohin Adamawa da Taraba ke ciki, sakamakon matsanancin zafin da ake fama da shi a yanzu, lamarin da yasa masu sayar da ruwan sha ke cin Karen su babu babbaka, su kuma yan kasuwa da magidanta suka koma amfani da na’urar dake bada hasken wutar lantarki.
Sai dai kuma matsalar na zuwa a dai dai lokacin da ake fama da rashin wutar lantarki cikin ‘yan kwanakin nan a cewar wasu mazauna yankunan da yanzu haka cikin wannan mawuyacin hali.
Kamar yadda masana ke cewa zafi na cikin matsalolin dakan jawo cutar sankarau da yayi sanadiyar asarar rayuka a wasu jihohin Najeriya. Mallam Muhammad Kabir, jami’in kiwon lafiya ne a Jalingo fadar jihar Taraba, ya gargadi wadanda ke kwana a daki ne da cewa su kula domin alamomin sankarau na zuwa ne da ciwon kai da zafin jiki mai tsanani, kuma zafi shine ke haddasa shi.
Alkaluman hukumomin kiwon lafiya a Najeriya na nuni da cewa ya zuwa yanzu fiye da mutune 300 ne suka mutu a bana sakamakon cutar sankarau, kuma fiye da dubu biyu suka kamu da wannan cuta dake da alaka da yanayin zafi.
Dr Fidelis Chagwa, likita ne a Asibitin New Botcham dake Yola, ya bayyana matakan da ake dauka idan har an kamu, kuma yace a hanzarta zuwa asibiti da zarar an ji alamun cutar.
Ya zuwa yanzu tuni wasu yankuna suka fara samun ruwan sama, yayin da wasu kuma har yanzu ko digon ruwa basu samu ba wanda hakan ke tilastawa talakawa kwanan waje sakamakon matsanancin zafi.
Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5