Matsalar tsaro da shirye -shiryen zabukan shekarar 2020 da 2021 da matsalar ambaliyar ruwa, sune mahimman batutuwan da Shugaban kasar Nijar, Issoufou Mahamadou da mazon musamman na babban Sakataran Majalisar Dinkin Duniya a kasashen Yammacin Afrika da kuma Sahel Mohammed Ibn Chambas suka mayar da hankali a kai a wannan ganawar.
Bayan ya gana da shugaban kasar ta Nijar Mohamed Ibn Chambas ya samu zantawa da manema labarai.
Ya ce, "Na yaba wa shugaban kasar Nijar, Issoufou Mahamadou game da yadda ya shirya babban taron kungiyar kasashen Yammacin Afurka CEDEAO ko ECOWAS yabon da kuma ya samu daga wajen sauran takwarorinsa, sannan mu samu musayar yawu game da matsalar tsaro - musamman hare-haren ta’addanci da ake ci gaba da samu a ‘yan kwanakin da kuma matsalar ambaliyar ruwa da ta haddasa asarar rayuka da dama da kuma kaddarori a jamhuriyar ta Nijar.”
Game da batun shirye-shiryen zabukan shekarar 2020 da kuma shekarar 2021, a Nijar Ibn Chambas ya ce "Zabuka ne masu mahimmacin gaske domin zasu bada dama a karon farko wani zababben shugaban kasa ya mika mulki hannu wani zababben shugaban kasa. Abu ne da zai shiga a cikin tarihin kasar nan”
Ganawar da aka yi tsakani manyan biyu, ta kuma tabo batun zabukan da sauren kasashen Yammacin Afrika biyar za su gudanar a wannan shekarar ta 2020, inda Ivory Coast da Guinea za su gudanar da nasu zabukan ne a cikin watan Octoba sannan Burkina Faso a cikin watan Nuwamba, Ghana da Nijar kuma a cikn watan watan Disamba.
Ga Yusuf Abdullahi da cikakken rahoton ta sauti:
Your browser doesn’t support HTML5