Fatai Owoseni, kwamishinan ‘yan sandan jahar Lagos, shi ne ya bayyana hakan a wajen wani taro da aka gudanar, inda yace cikin shekara guda da ta gabata an kashe mutane 246 da kuma sace motoci 542 tare kuma da kame wasu ‘yan fashi da makami kimanin 486.
Kwamishinan yace mutanen da aka kashe, kisan nasu na da alaka ne da ayyukan kungiyoyin asiri ko kuma fadace fadace tsakanin kungiyoyin matasa daban daban.
A cewa wani mazaunin jahar mallam Husaini Mani, har yanzu ‘yan sanda na karbar cin hanci da rashawa, kuma a duk lokacin da mutum yakai rahotan an sace masa abin hawa musamman babur ‘yan sanda basa tabuka komai aka.
Batun fashi da makami na daya daga cikin matsalolin dake fuskantar jahar Lagos, abin da kuma kwamishinan yan sandan yayi bayanin cewa ‘yan fashi da makami 46 aka kashe a lokacin fito na fito da jami’an yan sandan jahar. Yayin da kuma rundunar ta kama wasu mutane 38 da ake zargin cewa masu garkuwa da mutanen ne.
Daga karshe kwamishinan yayi kira ga al’umar jahar da su baiwa jami’an ‘yan sanda hadin kai don magance matsalolin tsaro a jahar.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin daga Lagos.
Your browser doesn’t support HTML5