Tabarbarewar sha'anin tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya na kara fadada, inda manyan birane ke ci gaba da daukan bakuncin ‘yan bindiga. Lamarin da ya sa mazauna jihohin Sokoto da Kebbi ke rokon Hukumomi akan su bayar da kulawar da ta kamata ga tsawon rayukan ‘yan kasa.
A baya a jihar Kebbi, yankin Zuru ne kadai ake ji da matsalar rashin tsaro sai gashi yanzu abin ya fadada zuwa wasu birane, domin a kwaryar garin Birnin Kebbi an fara samun ‘yan bindiga suna addabar jama'a.
Karin bayani akan: Kola Okunlola, 'Yan bindiga, jihar Sokoto, jihar Kebbi, Nigeria, da Najeriya.
Ko bayan hare-hare da ake kaiwa, an sace wata yarinya wadda aka sako ta bayan biyan kudin fansa, san nan kuma aka sake kai wani hari yankin Kalgo inda aka sace wata matar aure.
A yankin Bena na masarautar Zuru, har yanzu akwai sauran yan bindiga duk da yake an girke jami'an tsaro a yankin.
jihar Sokoto, ana samun rahotannin matsalolin ‘yan bindiga inda ko a wannan mako kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kamaldeen Kola Okunlola, ya gabatar da wadanda ake tuhuma da satar mutane su 17 wadanda aka kama tare da wasu masu aikata ayyukan ta'addanci.
To sai dai shugaban kungiyar banga a yankin Rabah dake Sokoto wanda ke fama da matsalolin rashin tsaron, ya ce a shirye suke su bayar da bayani idan jami'an za su kawo dauki wurin kakkabe sansanonin yan ta'addar.
Matsalar rashin tsaro dai ta mamaye yankunan arewacin Najeriya har jama'a na tunanin hukumomi sun gaza magance matsalolin.
Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.
Your browser doesn’t support HTML5