Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da tabbacin cewa za a kara samun sauki ga samarta da rancen tayar da komadar mata, kuma za a samar da karin sarari ga mata don shiga harkokin siyasa.
Shugaban ya ce sauran mukaman da aka bai wa mata sun hada da: Ministan Sufuri, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Shugaban Ma’aikatan Tarayya, Kwamitin Ma’aikatan Tarayya da Manajan Darakta, Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na Najeriya ( NPA).
Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
“Ina matukar alfahari da nasarorin da tsohuwar Ministar Muhalli kuma Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, da Fatima Mohammed Kyari a matsayinta na Daraktan din-din-din ta Kungiyar Tarayyar Afirka ga Majalisar Dinkin Duniya da kuma sabon zababben Darakta-Janar na Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Dr. Ngozi Okonjo-Iweala su ka yi."
“Tun daga lokacin na umarci Babban Mai Shari’a na Kasa da Ministan Shari’a tare da hadin gwiwar Ministan Harkokin Mata su hanzarta kaddamar da Kwamiti don magance duk wani nau'i na cin zarafin mata da yara kanana a kasar. Wannan kwamitin ya riga ya fara aiki, a cewarsa.