Matsalar Tsaro Ta Ta'azzara A Kasashen Yankin Sahel

Alkassoum Abdourahaman

A hirar su da wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma, Alkassoum Abdourahman wanda yake sharhi kan sha'anin tsaro, ya ce matsalolin 'yan ta’adda sun zafafa, a ‘yan kwanakin nan a kasashen Mali, Burkina Faso, da Jamhuriyar Nijar.

Masana sha’anin tsaro sun fara jan hankulan gwamnatocin kasashen Yankin na Sahel kan bukatar musanyar bayanai don ganin an yi nasarar rusa abubuwan da kungiyoyin ta’addancin yankin Afirka ta Yamma suka tsara da hadin gwiwar takwarorinsu na nahiyar Asiya.

A saurari cikakken hirar daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Matsalolin ' Matsalar Tsaro Ta Ta'azzara A Kasashen Yankin Sahel