Matsalar Tsaro: Gwamnatin Najeriya Za Ta Kirkiri Cibiyar Sojojin Hadin Gwiwa A Arewa Maso Yamma

Ministan Tsaron Najeriya, Badaru Abubakar

Ministan Tsaron Najeriya, Badaru Abubakar, ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis lokacin da ya kaiwa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ziyara a fadarsa dake gidan Sir Kashim Ibrahim, a wani bangare na rangadin da yake yi a yankin arewa maso yamma.

Nan bada jimawa ba ma’aikatar tsaron Najeriya za ta kafa wata cibiyar hadakar sojoji a shiyar arewa maso yamma mai lakabin “Operation Fansar Yamma”, a matsayin wani bangare na kokarin gwamnatin kasar na shawo kan kalubalen tsaron dake addabar yankin.

Ministan Tsaron Najeriya, Badaru Abubakar, ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis lokacin da ya kaiwa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ziyara a fadarsa dake gidan Sir Kashim Ibrahim, a wani bangare na rangadin da yake yi a yankin arewa maso yamma.

Manufar ziyarar ita ce kammala tsare-tsaren kaddamar da aikin wanzar da zaman lafiya mai lakabin “Operation Fansar Yamma”, inda shelkwatar tsaron Najeriya za ta kafa cibiyar hadakar sojoji domin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi yankin.

Badaru yace kafa cibiyar tsaron nada matukar mahimmanci wajen magance matsalolin ‘yan bindiga da ta’addanci da satar mutane da sauran nau’ukan laifuffukan dake da alaka dasu da suka daidaita yankin tsawon lokaci.