Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shettima Ya Kwadaitawa Masu Zuba Jari Yanayin Bunkasar Kasuwanci A Najeriya


Kashim Shettima (Facebook/Bola Ahmed Tinubu Support Group Germany)
Kashim Shettima (Facebook/Bola Ahmed Tinubu Support Group Germany)

A jawabinsa Shettima yace Najeriya da Sweden na da dadadden tarihin yin hadin gwiwa, musamman a fannonin kasuwanci da fasaha da ci gaba mai dorewa.

Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya bukaci masu zuba jarin kasa da kasa dasu ci gajiyar yanayin bunkasar harkokin zuba jari a Najeriya.

Mataimakin shugaban kasar yayi wannan kiran a yayin wata ganawa da ‘yan kasuwar kasar Sweden, a birnin Stockholm, a wani bangare na ziyarar yini 2 da yake yi a kasar.

A cewarsa, gwamnatin tarayyar Najeriya ta gudanar da muhimman sauye-sauyen dake sake fasalta yadda bunkasar tattalin arzikin kasar za ta ci gaba da dorewa, inda yace manufar gwamnatinsu ta “sake sabunta fata” za ta maida hankali ne a kan yadda za a samar da yanayin gogayya a kasuwanci ta yadda zai janyo masu zuba jari daga ciki da wajen kasar.

A jawabinsa Shettima yace Najeriya da Sweden na da dadadden tarihin yin hadin gwiwa, musamman a fannonin kasuwanci da fasaha da ci gaba mai dorewa.

Ya kuma zayyano irin damammakin da ake dasu a Najeriya, da suka hada da tsarin tattalin arzikin zamani da noma da makamashi mai tsafta da kanana da matsakaitan masana’antu, inda ya bayyana cewa Najeriya ta zamo kasa mai burin ci gaba, dake tafiya a kan dimbin damammakin da ci gaban masana’antu na 4 ya samar.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG