MATSALAR TSARO A Najeriya: An Maka Buhari A Kotu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Da Mataimakinsa Osinbajo Sun Gana Da Sifeton 'Yan Sanda

Tsohon dan takardar gwamna a Jamiyyar AAC ( African Action Congress) a Jihar Adamawa da Ke Arewa Maso Gabashin Najeriya, Alhaji Auwal Uba ya maka shugaba Mohammadu Buhari a kotu saboda cigaba da rike shugabanin tsaron kasar duk da cewa sun gaza shawo kan matsalar tsaro da ke addabar Kasar.

A wata hira ta musamman da yayi da muryar Amurka a Abuja, tsohon dan takaran ya ce ba shugabanin tsaron kadai ya Ke so a cire ba.

Alhaji Auwal A. Uba ya shigar da karar a gaban babbar Kotun Taraiyya da ke Abuja inda ya roki kotun da ta umarci shugaba Buhari da ya sauka daga kan kujerar mulki da shi da dukan shugabanin hukumomin tsaron kasar baki daya.

dole-ne-yan-sanda-su-sake-salo-wajen-yaki-da-yan-bindiga-igp

zamu-ga-bayan-masu-garkuwa-da-mutane-don-neman-kudin-fansa---burutai

wasu-yan-najeriya-na-alakanta-matsalar-tsaro-da-sakacin-gwamnati

A.A.Uba ya ce ya dauki matakin ne a madadin shiyar Arewa wadanda ke fama da rashin tsaro tun tsawon shekarun da Shugaban Buhari ya ke mulki.

Uba ya ce baya ga wadannan bukatun kuma, yana son gwamnatin tarayya ta biya Naira Biliyan 100 ga wadanda abin ya shafa a matsayin diyya.

Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Tsaro a Sokoto

Daya cikin Shugabanin kungiyar Muryar talaka Saleh Bakoro sabon feggi ya ce Shi bai amince da Kiran shugaba Buhari ya sauka ba, amma yana so a chanja Shugabanin Hukumomin tsaro saboda sun dade akan mukaman nasu har sun zama babu sauran dabarun kawar da 'yan ta'adda da masu tada kayar baya.

Shi Kuwa kwararre a fanin Shari'a Barista Abdulqadir Alhaji Sani ya ce shigar da kara akan wani abu da dan kasa yake ganin bai gamsu da shi ba, dama ce da dokar kasa ta bayar, saboda haka wannan yunkuri da aka yi na shigar da kara saboda tsaro, ya yi daidai.

Babban Hafsan Sojojin Najeria Janar Tukur Yusuf Burutai Ya Ziyarci Sansanonin Sojojin Najeriya

Za a saurari karar a ranar 18 ga Watan Maris na shekara 2021.

Saurari cikakken rahoton Madina Dauda cikin sauti

Your browser doesn’t support HTML5

MATSALAR TSARO A Najeriya: An Maka Buhari A Kotu:3:00"