Cikin ire iren rugujewar gine ginen da aka samu a Najeriya, akwai rugujewar wata Majama’a dake birnin Kaduna a shekara ta 2011, haka kuma cikin watan Disambar shekara ta 2014 ginin makarantar Firamare ta Abu Ni’ima dake Bukuru a jahar Plateau ya ruguje.
Masu kididdiga dai sunce cikin tarihin rugujewar gine gine a Najeriya babu wanda ya kai wanda ya faru a birnin Lagos na Majami’ar TB Joshu’a da ya afka kan masu ibada kusan 300, haka kuma sai gashi ranar Asabar din da ta gabata wata Majami’a ta kuma rusowa da saura kiris ta ritsa da gwamnan jahar Akwa Ibom a birnin Oyo.
Masanin gine gine Injiniya Mohammed Kyari Sandabe, yace mafi akasarin abubuwan da ke kawo rushe-rushen gine gine sune kayan da akayi amfani da su wajen ginin, da suka hada da siminti da yashi da karafuna da dai sauransu. Gini yana da tsari wanda idan har za a bi, a kuma guji amfani da kayayyakin da tsarin ya hana to za a sami saukin samun rugujewar gini gine.
Shi kuma kusa a kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya Injiniya Kamsulum Alhaji Bukar, cewa yayi Injiniyoyin jabu da sukayi kakagida a cikin sana’ar gine gine a Najeriya, suna taka rawa wajen samar da gidaje marasa inganci da daga bisani kan ruguzo.
Domin karin bayani saurari ciakken rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5