Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Mu Ka Ce a Janye Shirin Hana Shiga Da Motoci Najeriya- Salame


Masu motoci a wani yankin Najeriya
Masu motoci a wani yankin Najeriya

Majalisar dokokin Najeriya na ci gaba da kare kudurin dokar da za ta sa a janye shirin hana shiga da motoci ta iyakokin kasar.

Hon. Abdullahi Balarabe Salame, wanda ya fara gabatar da kudirin, ya ce dokar za ta iya janyo asarar rayuka.

“Duk lokacin da aka hana mutane abin da shi su ke so kuma su na ga su na bin sa bisa ka’ida, za su yi kokarin yi ba bisa ka’ida ba, hakan kuma zai kai ga rasa rayuka.” In ji Salame.

A cewar Hon. Salame, za a iya samun arangama tsakanin masu safarar motocin da jami’an tsaro inda za a iya samun asarar rayuka har da na jami’an tsaron.

A makon da ya gabata ne, shugaban hukumar kwastam na kasa, Hamid Ali, ya ce daga ranar 1 ga watan Janairun 2017 dokar hana shiga motoci ta kasa za ta fara aiki.

Hukumar ta kwastam ta ce gwamnatin na tafka asarar wajen bari a ana shiga da motoci ta kasa, amma idan ana shiga da su ta ruwa gwamnati za ta fi samun kudaden shiga.

Domin jin karin bayani saurari rahoton wakiliyar sashen Hausa na Muryar Amurka, Medina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:02 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG